12 Maris 2026 - 19:48
Source: ABNA24
Jagora: Zama Akan Kujerar Manyan Shugabanni Biyu, Babban Khomeini Da Shahid Khamenei Yana Da Wahala Gareni

Sakon Farko Na Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci yanki na farko

Sakon Farko Na Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai.

بسم الله الرّحمن الرّحیم

مَا نَنسَخْ مِنْ ءَآیَةٍ أَوْ نُنسِهَا نَأتِ بِخَیْرٍ مِّنْهَآ اَوْ مِثْلِها.

اَلسَّلامُ‌عَلَیکَ یا داعِیَ‌اللهِ وَ رَبّانِیَّ آیاتِهِ، اَلسَّلامُ‌عَلَیکَ یا بابَ‌‌اللهِ وَ دَیّانَ دینِهِ، اَلسَّلامُ‌عَلیکَ یا خَلیفَةَ‌اللهِ و ناصِرَ حَقِّهِ، اَلسَّلامُ‌عَلیکَ یا حُجَّةَ‌ا‌للهِ وَ دَلیلَ اِرادَتِه؛ اَلسَّلامُ‌عَلیکَ اَیُّهَا المُقَدَّمُ المَأمُول؛ اَلسَّلامُ‌عَلیکَ بِجَوامِعِ السَّلام؛ اَلسّلامُ‌عَلیکَ یا مَولایَ صاحِبَ الزَّمان.

A farkon jawabi, dole ne in yi ta'aziyya ga Shugabana, Allah ya Gaggauta bayyanarsa, dangane da shahadar babban jagoran juyin juya halin musulunci, abin kauna Khamenei, mai Hakima, kuma ina rokon addu’ar alhairi daga gareshi ga kowa ne daya daga cikin babbar al'ummar Iran, dama dukkan musulmin duniya da dukkan masu hidimtawa musulunci da juyin hali da wadanda suka sadaukar da kansu da wadanda su aki saura na shahidan harkar Musulunci, musamman yakin baya-bayan nan, da ma ni kaina makaskanci.

Kashi na biyu na jawabina ga babbar al'ummar Iran ne. Da farko dai, dole ne in yi bayani a takaice a kan zaben da Majalisar Kwararru suka gudanar. Wannan bawan naku, Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei, ina tare da ku a daidai lokacin da ku ta gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci, a lokacin da aka sanar da ni sakamakon kuri'ar da aka yi na babban taron kwararru. Yana da wuya a gare ni in zauna ga wurin da manyan shugabanni biyu, Babban Khomeini da Shahid Khamenei. Domin wannan kujera tana da tarihin zama ga wanda, ya key a shafe fiye da shekaru 60 na gwagwarmaya a kan hanyar Allah da kawar da kai ga kowane nau'i na jin daɗi da jin sauki, ga wanda ya zama mabubbugar haske da fitacciyar fuska ba kawai a wannan zamani ba har ma a cikin tarihin wadanda suka shugabanci wannan ƙasar. Kuma Dukan rayuwarsa da nau’in mutuwarsa suna cike da ɗaukaka sakamakon dogaro da gaskiya.

Na sami damar ziyartar gangar jikinsa bayan shahadarsa. Abin da na gani wani kaffaen dutse ne mai ƙarfi kuma na ji cewa ya dunkule lafiyayyen hannunsa yana mai garkuwa da shi. Mutanen da suka san abubuwa daban-daban na halayensu ya kamata su faɗi abubuwa na dogon lokaci (na abubuwan d suka sani danagne da shi). A wannan lokacin, zan takaita da wannan zan bar cikakkun bayanai zuwa wasu yanayi da suka dace. Wannan shi ne dalilin wahalar zama kan kujerar shugabanci a bayan irin wannan mutum, amma yana yiwuwa a iya cika wannan tazarar kawai da taimakon Hazrat Haqq da taimakon ku, jama'a.

A ciki ga ba da bayani na, zanje ga batu da yake da alaka da asalin wajibi na kai tsaye. Wanna batun kuw shi ne, daya daga cikin fasahar shahid jagora da kuma babban magabacinsa shi ne ya gabatar da mutane a kowane fanni cikin basira da kuma wayar da kansu akai-akai, da kuma dogaro da karfinsu a aikace. Ta wannan hanyar, sun aiwatar da ainihin ma'anar Jamhuriya da Jamhuriyyat, kuma sun yi imani da ita daga tsatson zuciya. Wanda an ga tasirin wannan al'amari a cikin 'yan kwanakin nan da kasar ta kasance ba ta da jagora kuma ba tare da babban kwamanda ba. Basira da Hankalin babbar al'ummar Iran a cikin waki’ar na baya-bayan nan ta hanyar juriya da jajircewa da kasancewarsu sun karafafa da kwadaitar da masoya da jefa abokan gaba cikin rudi. Ku ne kuka jagoranci kasar kuma kuka ba da tabbacin ikonta. Ayar da na nakalto a farkon wannan rubutun na nufin cewa babu wata aya daga ayoyin Allah da aikinta ya kare ko kuma ka manta da ita face sai daga bangaren Hazrat Haq jalla-ala, ya kawo kamarta ko wacce ta fita (ya maye wurinta da ita)…..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha